Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutum 9 Sakamakon fadawar wata Mota cikin ruwa a rafin Gwarzo da ke nan Kano,
Me magana da yawon hukumar PSS Saminu Yusuf Abdullahi ya tabbatar da haka a yau lahadi ga manema labarai, inda ya ce "Tsautsayi ya Kuma ritsa da mutum 12 wanda dukkaninsu ba mu samu sunayensu ba daga cikin wadanda tsautsayi ya rutsa da su akwai Yara kanana yan kimanin waya shida guda 2. Akwai Kuma mata manya guda 4 wadanda shekarunsu ya kama daga shekara 30 da 28 da 27 da 25,
"Sannan kuma akwai Maza wadanda tsautsayinbya hada da su 6 wadinda ya hada da Yan kimanin 48 45 42 40 da kuma shekara 35 da kuma 28
Yusuf Abdullahi ya cigaba da cewa "Da taimakon Allah da taimakon jami'anmu da kuma masunta, mun samu nasarar tseratar da mutum 3 a raye"inji Yusuf Abdullahi
Sannan ya ce sun sun tseratar da mutum 9 wadanda basa cikin hayyacinsu a yayin hadarin.
Tuni dai wadanda suka jikkata da lamarin ya shafa aka kaisu asibitin Gwarzo domin ceto rayuwarsu.


