KANYWOOD:Muna da kyayyawar alaka da Maryam Yahaya amma ba soyayya muke ba--Shamsu Dan'iya

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Fitaccen Jarurumi a masana'atar Kannywood wato Shamsu dan'iya ya musanta jitajitar da ake yadawa dangane da cewa wai zai auri Maryam Yahaya, 

A yan kwanakin nan dai kafafen sada zumumta na Social Media da wasu Jaridun kasar nan sun ta yayata cewa Shamsu Dan iya zai an gwance da Jaruma Maryam Yahaya, 
Shamsu Dan iya da a yanzu aka fi kira da Hisham, ya ce daga lokacin da aka fara yada jitajitar zuwa yanzu a kodayaushe yana karba kira daga wajen mutane Daban-dadan.

A wata tattaunawa da ya yi da Jaridar Inuwar Labarai Dan'iya ya ce abin ya samo asali ne tun lokacin da suka yi tafiya zuwa kasar Dubai yayin daukar Shirin Fim din alaka an gansu a Hotuna da dama a can,
Kazalika ya cigaba da cewa "Mafiyawa idan muka je taruka haka akwai masu bibiyarmu da masu daukar hoto da yan jarida ana daukar hoto ana yadawa, ita kuma duk lokacin da muka hadu za ka ga cewa akwai abin da muke tattaunawa to a daidai lokacin da muke tattaunawa ne zaka ga an dauke hotuna sai aita yadawa, to shiyasa mutane suke alakanta abin da cewa muna soyayya ko abinda ya yi kama da haka, Amma Babu wannan maganar, Maryam Yahaya Kanwata ce muna mutunci da ita" . Inji Shamsu Dan iya

In dai baa manta ba ko a yan watanni baya an dinga yayata cewa Shamsu dan iya zai auri yar maigidansa Ali Nuhu wato Fatima Ali Nuhu, wanda shi ma ya musanta.

Wannan dai ba sabon abu ba ne wajen yada Jitajita irin wannan, musamman ma a masana'atar Fim ta Kannywood.

Post a Comment

Previous Post Next Post