Wata matar aure, Amina Muhammad, a ranar Juma’a ta maka mijinta, Salisu Mohammed, a gaban wata kotun gargajiya da ke Nyanya, Abuja, bisa zargin auren wasu mata biyu a asirce.
Mai shigar da karar wacce ke zaune a unguwar Mararaba, Abuja, ta yi wannan zargin ne a cikin karar da ta shigar a kan mijinta.
Ta yi zargin cewa mijinta ya auri wasu mata guda biyu a asirce kuma ya yi musu hayar gidaje a wurare daban-daban a Abuja, yayin da ya bar ta a Mararaba.
Ta ce mijin nata ya sha yi mata barazanar cewa zai sake ta tare da koron ta da karfi daga gidan aurenta.
Ta kuma shaida wa kotun cewa mijin nata ya shafe sama da shekaru biyar yana tauye mata hakkin aurenta.
Misis Muhammad ta roki kotun da ta sake ta, inda ta ce rayuwarta da ta ‘ya’yanta ma cikin garari.
“Ina rokon wannan kotu mai daraja da ta ba ni saki da kuma hanyar samar mana da kula mai kyau ni da ‘ya’yana, saboda mijina yana yi mani barazana yana kuma alfahari da cewa zai kore ni daga gidansa ta karfi idan ban fita salum alum ba,” inji ta.
Sai dai wanda ake kara wanda ya halarci kotun ya musanta zargin.
Alkalin kotun, Doocivir Yawe, ya dage ci gaba da sauraron karar domin haduwa a zama na gaba.
