Kungiyar Malaman Tsangaya Reshen Jihar Yobe sun gudanar da taro na wuni guda a Garin Damaturu babban birnin jihar domin fadakar da membobunsu Muhimmanci yankar Katin Zabe.
Taron Wanda ya samu halarta wakilai daga Kananan Hukumomi 17 dake fadin jihar ya dama baki daga jihohin Borno,Gombe da Jigawa.
Dayake Jawabi Babban Bako Kuma Shugaban Kungiyar Malaman Tsangaya Ta Kasa Gwani Ibrahim Abubakar Mai Bindiga ya nuna Jin dadin sa Kan hadin Kan da membobin kungiyar suke bayarwa.
Duk Wanda Yasan tarihin Tsangaya Yasan Almajirai mutanene masu nizami da bin Shugabanci Wannan tasa Mike fadakar da Yan uwanmu su San suwa zasu zaba domin daga darajar Almajirai da Malaman Tsangaya.
Dayake Jawabi godiya Shugaban Kungiyar Reshen Jihar Yobe Gwani Muhammad Abubakar ya nuna jin dadinsa ga irin nimijin kokarin da Shugaban Kungiyar na kasa yake yi tare da membobinsa wajen shiga loko da sako na Kasarnan.
Gwani Muhammad ya Kara da cewa Zuwa Yanzu Muna da adadin Almajirai da Malamai Wanda sukayi rijista dubu casain da Dari bakwai da sittin da uku Wanda suke a shirye domin zabar Wanda zai kawo musu cigaba a tafiyar Tsangaya.
Shima anasa Jawabin Dr. Abubakar Maje Malami a jami'ar Sule Lamido dake Kafin Hausa ya bayyana irin Shirin da Kungiyar take dashi domin gabatar da Bill a majalisar tarayya Wanda zai taimaka Almajirai da Mallansu.
Dr. Abubakar Maje ya Kara da cewa Malaman Qur'ani sun cancanci abasu takardar shaidar Kammala karatu Wanda zasu gabatar da ita koina a fadin Duniya.
A karshe aka gabatar da addua tare da karatu Qur'ani gami da daukan hotunan domin tarihi.
