![]() |
Wasu ‘yan uwa, kimanin mutane 11 sun mutu sakamakon cin abinci mai guba a yankin Ikobi da ke karamar hukumar Apa ta jihar Benue.
Mazauna kauyen sun bayyana cewa ’yan uwan gida gudan sun mutu ne bayan da ake zargin sun ci abinci da ya gurbata da sinadarai masu illa.
Mutanen 11 da abin ya shafa su ne: Adi Ale, Ochefije Ojo, Maria Ojo, Aipu Ochefije, Aboyi Ngbede Ochefije, Mary Ochoyoda, Ehi Abu, Blessing Abu, Peace Ochoyoda, Ojochono Daniel da Favor Edoh.
An tattaro cewa yayin da shida daga cikin wadanda abin ya shafa suka mutu a rana daya, sauran biyar sun mutu kwanaki kadan bayan haka.
Daya daga cikin ‘yan uwa da suka rasu, Ochoyoda Abu, ya rasa matarsa (Maryamu) da ’yan’uwa mata biyu (Ehi da Blessing) da kuma ‘yar (Assalam).
Farfesa Mohammed Adah, basaraken al’ummar Ikobi, ya ce makamancin irin wannan lamari ya taba faruwa a watan Satumba.
Ya ce, an kara tabbatar da cin gubar na su ne bayan samun karin mutum biyar daga cikin wadanda abin ya shafa suka mutu a rana guda a cikin al’umma, ya kara da cewa an gayyaci kwararru daga ma’aikatar lafiya ta jihar domin su binciki musabbabin mutuwar ta su.
Adah ya ce har yanzu ba a bayyana sakamakon binciken ga al’umma ba.
An bayyana cewa, akwai wadanda kuma suka yi rashin lafiya bayan sun ci abincin kuma an kai su asibiti. Kazalika, a bangare guda bayan basu kulawa sun sami lafiya tare da komawa cikin ahlin su.
Likitan cututtukan da ke jihar, Dokta Sam Ngishe, bai amsa kiran da aka yi masa ta wayar tarho ba don jin ta bakinsa game da binciken da ake yi a kan lamarin ba har ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.
Sai dai jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda (PPRO), SP Catherine Anene, ta ce wadanda abin ya shafa sun mutu ne a ranar Litinin da ta gabata, 14 ga watan Nuwamba, ta kara da cewa bakwai daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su an tabbatar da mutuwarsu a rana daya kadai.
Anene ta ce, “Kusan watanni uku da suka wuce, wani ya mutu a wannan gidan, don haka a ranar 14 ga watan, wata mata ta je gidan, ta share gidan sannan ta kwashe kayan abinci ta dafa, bayan sun ci ne mutane 12 suka kamu da ciwon ciki.
“A wannan rana mutane bakwai ne suka mutu sannan biyar aka kai su asibiti kuma yayin da akai nasarar ceto rayukan su. Kawo yanzu dai ana ci gaba da bincike.”
Wani tsohon kwamishinan matasa da wasanni na jihar, Kwamared Ojotu Ojema, ya ziyarci iyalan wadanda suka rasu a Oleg’oke da ke Ikobi a ranar Lahadin da ta gabata don jajanta musu.
Ojema a cikin sakon ta’aziyyarsa ga Iyalan Ayigoche da Iyalan Ayigoga ya bukace su da su fauwala lamarin wa Allah.
Da yake mayar da martani, wani mai rikon mukamin Basaraken Ikobi, Cif Musa Audi, ta bakin Sakataren Majalisar Gargajiya ta Ikobi, Abogonye Ochola John, ya godewa Ojema da ya zo yayin da yake ba da labarin irin bala’in da ya addabi al’ummar ta su.
John ya yi iƙirarin cewa sun yi kokarin rufe abin d9n gudun tashin hankali, a cewarsa, ba din an sami taimakon Allah ba, da an samu tashin hankali gaba daya yayin da lamarin ya koma zato, kiyayya da zargi a tsakanin iyalai a cikin al'ummar yankin.
