Matan Da Matasan APC Sunyi Wa Tinubu/Shettima Alkawarin Kuri'u Miliyan 40.

Daga Abdulnasir Yusuf Ladan

Jam'iyyar APC mai mulki a ranar alhamis ta sha alwashin cewa mata da matasa a Najeriya za su bayar da kuri'u miliyan 40 ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Bola ahmed Tinubu da abokin takarar sa, Alhaji Kashim Shettima, a zaben 2023. 

Da take jawabi a taron mata na yakin neman zaben shugaban kasa a ilorin, shugabar mata ta jam’iyyar ta kasa, Binta Edu, ta bukaci mata da su yi watsi da duk wani abu da ke damun su, inda ta kara da cewa, “yarjejeniyar ita ce samar da kuri’u Miliyon 40 wa Bola ahmed tinubu da kashim shettima. 

“Muna da babban dan takara Bola Tinubu da kuma abokin takararsa, su biyun za su kawo nigeria cikin mafarkinta. wannan ne lokacin da za a hada kai,” in ji ta.

Edu ta kuma yi alkawarin cewa za a ba wa mata fifiko, sannan ta bukaci mata da kada su shagala da manufofin da suka sanya a gaba. 

Har ila yau, uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta bazama wajen gudanar da yakin neman zabe gida-gida da kuma jiha zuwa jiha domin samun nasarar Ahmed Tinubu da Kashim Shettima a zaben 2023 mai zuwa. 

“Shekaru bakwai da suka gabata, mun yi abu iri daya kuma sakamakon ya haskaka kowa ya gani. don haka nasarar da jam'iyyar APC ta samu a shekarar 2015 na daya daga cikin irinsa a tarihin zabe a kasar. 

Ba a kalubalanci sakamakon a kotu ba ko kuma a ra'ayin jama'a. tarihi ya kusa maimaita kansa.

Mata da matasa na nigeria za su maimaita abu iri daya a zaben 2023. a karkashin jam'iyyar APC, an tabbatar da makomar mata da matasa mu a matsayinmu na mata za mu zabi jam’iyyar mu, APC. 

Ta cigaba da cewa APC jam'iyya ce ta zaman lafiya da ci gaba, tana gudanar da yakin neman zabenta ba tare da kisa ba sabanin sauran jam’iyyun siyasa, sai dai jajircewa, hada kai da hadin kan matasanmu. 

Muna son mata da matasan mu su kasance a karkashin inuwa daya don isar da Tinubu/Shettima a 2023. 

A jawabinta a wajen taron, uwargidan dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi alkawarin tsayawa tsayin daka a bayan mijinta. 

“Mu mata, muna goyon bayan mazajenmu don tallafa wa marasa galihu ta hanyar kasuwanci. domin shugabancin Tinubu/Shettima, yana nufin  goben Nigeria mai kyau. 

 Shi ma da yake jawabi a wajen taron, gwamna Abdurrahman Abdulrazaq na jihar kwara ya ce, duk da cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC bai gama cika ba, amma zai samu goyon bayan jama’ar jihar saboda “tabbataccen tarihinsa a matsayinsa na mutum” .

Inuwar Labarai RPT 001

Post a Comment

Previous Post Next Post