TIRKASHI: Yayi ma diyar Surukin sa fyade a dakin Mahaifiyar Shi.



Daga Yusuf Hamisu 

An gurfanar da wani Mutun mai shekara 30 da Haihuwa mai suna Anas Ishaka wanda ke Unguwar Sabuwar Kofa cikin garin Katsina a gaban wata Kotun Magistrate ta Shida ( 6) da ke Jahar Katsina akan zargin ya yi ma wata karamar Yarinya mai Shekaru 14 Fyade (Rape) a kuma cikin dakin mahaifiyar shi.

Binciken Yan Sanda a matakin farko da aka gabatar da kara ya shaida ma Kotun cewa sun samu Labarin ne bayan da Mahaifin Yarinyar ya kai korafi a Babban Ofishin Yan-sanda dake cikin Birnin Katsina (CPS) a ranar 28 ga Wata September 2022 akan cewa wani yayan matar shi wato Suriki, ya yi ma Diyar shi Fyade a lokacin da Ita matar ta aiki Yarinyar zuwa gidan su.

Shi dai wannan Fyade da ake zargin Anas Ishaka ya aikata ya saba ma sashe na 254 acikin Kundin Dokar Katsina state Panel Court Law, 2021.

 An dai daga sauraron wannan Shari’a zuwa ranar 22 ga watan December 2022.
Fyaden dai da Anas Ishaka ya aikata yayi sanadiyar mutuwar Aure tsakanin Kanwar Anas da kuma Mahaifin ita Yarinyar da ake zargin yayi ma Fyaden.
 Ahalin yanzu dai Alkalin Kotun ta bada umarnin acigaba da tsare Anas Ishaka agidan Yari.

Inuwar Labarai 

Post a Comment

Previous Post Next Post