Gobara Ta Tashi A Kasuwar Singa Da Ke Kano
Yanzu haka gobara ta tashi a wani shago da ke babbar kasuwar sayar da kayan masarufi wacce aka fi sani da Singa da ke Kano.
Wakilinmu da yaziyarci wajen ya ce wani shagon da ake sayar da biskiti da alawoyi ne ya kama da wutar.
Yanzu haka dai jami’an hukumar kashe gobara na wajen suna ta kokarin kashe wutar.
Muna tafe da karin bayani…
Tushe Aminiya

