Daga Abdulnasir Yusuf Ladan
Jami'an 'yan sandan jahan katsina sun kama wata mata mai suna Maryam Habibu a ranan juma'a da ta gabata.
Ana zargin yarinyan da jefa dan tsohon mijinta mai suna Jamilu Rabi'u mai shekaru 4 a cikin rijiya.
Kakakin Rundunan 'yan sandan jahan katsina SP Gambo Isah yace, wadda ake zargin taje gidan tsohon mijin nata ta lallaba yaron zuwa wani wuri da ke kusa tajefa shi a cikin rijiyan ta kashe shi.
Yayin da maryam take zantawa da manema labarai tace, tunda farko tayi amfani da fartanya kan matan mijinta ta farko kuma haryanzu shari'an tana nan a kotu.
Inuwar Labarai RPT 001
Tags:
IFTILA'I
