An Sace Wayoyin Mutane Sama Da Mutum Dubu A Babban Taron PDP Na Jahar Katsina

Daga Wakilinmu

A ranar Talatar da ta gabata aka yi babban taron kaddamar da neman takarar kujerar shugaban Kasar Najeriya a Jam''iyyar adawa ta PDP, wanda da Alh Attitu Abubukar Turakin Adamawa yake yi.

An gudanar da taron a babban Filin Wasa na Muhammad Dikko Stadium dake cikin Birnin Katsina, an fara gudanar da taron da misain 10:00 na safe, taron ya samu halartar 'ya yan kungiyar daga koina a fadin Najeriya, taron ya kunshi Maza da Mata, Matasa da Tsoffafi.
Mawakan Gargajiya a bangaren Hausawa sun samu wuri na musamman, yayin da mawakan Siyasa, tare da masu shirya Finafinan Hausa sun kayatar da taron, ta bangaren 'Yan Kudu ma ba'a barsu a baya ba, fara daga yan kabilar Ingo, Tube, Nufawa Gwarawa da Yarbawa sun sun baje kolin wakokinsu da al'adasu.

Duk yawan Mutanen da aka tara ba'a ga tsohon Gwamnan Jahar ta Katsina Alh Ibrahim Shehu Shema ba da sauran Mutanen da suka goya masa baya, yayin da wasu masana siyasa ke alakanta hakan da "rikicin da jam'iyyar take fama da shi na cikin Gida, shi ne makasudin rashin ganinsu har ma da tsohon shugaban na Jam'iyyar"

Sama da mutum dubu goma 95,000 da biyar suka chanza sheka daga jam'iyya mai mulki zuwa jam'iyyar adawa ta PDP, masu masana siyasa na alakanta hakan da cewa "Mutane sun gaji da wannan mulkin na APC saboda rashin tsaro, tsadar abinci, da wahalar rayuwa da ake fama da ita a koina, " wasu kuma na cewa kawai sun gaji da mulkin na APC saboda tsadar Man Fetir da aka fama da ita saboda Mai na daga cikin abubuwan da Shugaba Buhari yace zai magance amma har yanzu kwalliya ta kasa biyan kudin sabulu.

Abun mamaki ba'a gama taron ba sai da aka sacewa sama da mutum dubu wayoyi, duk inda ka zagaya magana daya zaka ji ita ce satar wayar Salula, abun mamaki wasu ma an yanke su da Wuka, wasu kuma Matasa na guje guje ko a gansu gungu gungu suna tafiya ko suna guje, cikin nasu gudun wasu ke kwatar waya wasu kuma na bin Mutane da gudu, mata da mata, tsofaffi da kananan yara sun rasa wayoyinsu kamar yadda wakilinmu ya rasa wayoyi biyu ya kuma sheda mana cewa ban da shi ya ga sama da mutane 50 da abun ya shafa, yace kuma a gabanshi aka kwacewa wani dan Jarida waya.

Post a Comment

Previous Post Next Post