Buri na shi ne na buga kwallo a Raal Madrid da kasa ta Nigeriya--Abdulmajid Nana

Daga Ibrahim Hamisu

A daidai wannan lokaci Inuwar Labarai ta karbi bakuncin matashin dan Kwallon kafan nan mai suna Abdulmajid Bello da aka fi sani da Abdulmajid Nana da ya ke taka leda a Kulob din Capo do Leuca FC da ke kasar Italiya, Abdulmajid Nana wanda dan asalin jihar Kano ne, za ku ji cikakken Tarihinsa da kuma irin fadi tashin da ya yi har ya kai ga fita kasar Italiya. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Ko za mu iya sanin cikakken suna?

Suna na Abdulmajid Bello, Amma anfi sanina da Abdulmajid Nana

Za mu so ka gabatar mana da takaitaccen tarihinka?

An haifeni a unguwar Gwammaja housing estate Dala LG Kano Ranar 13 /10/ 2002, Amma iyaye yan Danbatta ne, sannan na taso a Gwammaja Housing estate Dala LG Kano, sannan nayi makarantar Dala primary da ke cikin karamar kukumar Dala, sannan nayi makarantar kings college da ke Kurna m.
Cikin ikon Allah da ga shi na tsince kaina a cikin manyan kungiyoyi a kasashe turai.
Me ya baka sha'awa ka shiga harkokin wassanni?

Abinda ya bani shaawa na shiga harkokin wasanni shi ne, Gani nayi da mu dinga zuwa muna biyar kudi muna kallan turawa, to ai gwanda muma muyi kokari muma mu shiga Dan muma turawa da Yan uwanmu su dinga kallan mu kamar yanda ake kallan su.

A wace shekara ka fara buga Kwallon kafa?

Na fara Kwallon kafa a shekarar 2009.

A wane kulub ka fara buga Kwallo?

Kulub di na na farko shi ne Liverpool FC Kofar Ruwa. Sai Allazi Manchester united, Kano. Sai na koma Pessi Acadamy, Kano, sai Kulob din Kwankwasiyya Acadami, Kano, sai Ganduje FC Kano, sai Pryme Football Acadamy Abuja, sai Sky soccer Academy Sweden, Galatiana FC Italiya, sai Ctropiano FC Italiya, sai Kuma Capo di leuca FC da ke kasar Italiya wanda na ke a halin yanzu.

A wane mataki Kulob din ka ya ke a halin yanzu?

kulab dina yana matakin Seria D na kasar Italiya.

Wadanne irin nasarori ka samu daga lokacin da ka fara harkokin Kwallon kafa zuwa yanzu?

A gaskiya nasarori da na samu ba za su kirgu ba, a takaice abinda zan iya tunawa shi ne na tsaya da kafata, sannan na taimaki yan uwana da abokan arziki, sannan dalilina wasu sun samu aikin Gwamnati, Kuma ta dalilin kwallon kafa na ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ido da ido, sannan Dalilin kwallon kafa na yi yawo a duniya, kamar irin su kasar Cameron, Italy, France Malta, Morocco, Sweden da kuma kasar England London.

Wane irin kalubale ka fuskanta kafin ka kai ga wannan mataki navsamun babban Kolub a kasar Italiya

Kalubale da na fuskanta, guda daya shi ne, sanda Ganduje Bebis FC muna training a filin Sani Abacha stadium, kafin na fita kasar Italy. Wata rana idan bani da kudin mota, to a kafa nake Tafiya da gudu har Sani Abacha stadium bayan an idar da sallar Asuba, har mutanen unguwar mu suke cewa ai ni Dan wahala ne, Ina wahalar da kaina Ina zuwa Sani Abacha stadium a kafa tin Daga Gwammaja Housing Estate Dala, to abin yana yi min ciwo a cikin raina, amma akwai wani abokina sunansa Sunusi Henry a Gwammaja ya ke, to shi kadai ne yake kwantar min da hankali, yana bani shawara akan na ci gaba da zuwa training a kafa, wataran sai labari.
To yau gashi maganar sa ta tabbata, yau ni Abdulmajid Bello nake buga Kwallon kafa a kasar Italiya.

Duba da cewa kai kadai ne dan kasar Nigeriy a culub din ku ya kake wajen gudanar da zamantakewa tsakanin ka da Yan kulub dinka?

Gaskiya Alhamdulillah, har yanzu ban samu wata matsala ba, saboda suna Sona sosai, sannan suna Jana a jikin su,

Mene ne burinka a wannan harka ta Kwallon kafa?

Burina in Sha Allah, naga na buga Kwallo a irin kungiyar kwallon kafa ta Juventus ko real Madrid ko Chelsea, sannan Ina da burin naga na bugawa kasata Nigeriya world cup,. Kuma na ciyo mata shi.

Wadanne hanyoyi kake gani zaa bi wajen inganta harkokin wasanni a Nigeriya?

Hanyoyin da za abi shi ne, mu dinga bude football academy, wato Academy na yara yan kasa da shekara 7 zuwa 17, sannan a basu kulawa sosai, sannan duk wanda ya cancanta to choach ya bashi dama , kar abi alfarma aje a dauko wanda bai cancanta ba a sashi, saboda babansa mai kudi ne, ko kuma wani ne a Gwamnati.

Wane ne maigidanka?

Mai gida na shi ne (Patrick akosubo) Tsohon group Captain na Sojan Nigeriya Nigeria air force officer sannan shugaban pryme football Academy Abuja da kuma jihar BENUE.

Post a Comment

Previous Post Next Post