Daga Comr Nura Siniya
Wasu fusatattun matasan Yarbawa ɗauke da makamai sun tare ayarin motocin Ɗan takarar shugaban ƙasa Asiwaju Bola Tinubu sun farfasa masa gilassan motoci da yimasa ihun bamayi tare da raunata ƴan jarida 2 akan hanyarsa ta zuwa gidan Sarkin yarabawan Oba na Jihar Lagos.
A rahoton da muka samu matasan sun farfasa gilasan ayarin motocin Bola Ahmad Tunibu da duwatsu sun raunata Ɗan Sanda da ƴan Jaridu guda biyu.
A lokacin da Lamarin ya faru harin bai shafi Bola Tinubu ba saidai da ƙyar dai Jami'an tsaro suka tseratar dashi izuwa Gidan Sarkin yarabawan Oba na Jihar Lagos.
Afkuwar lamarin ya girgiza jama'a ganin yadda aka ci zarafin Ɗan takarar tare da yimashi bore a mahaifarshi ta haihuwa.
A gaskiya irin wannan siyasa bata dace da rayuwar matasa domin ba zata haifar masu da makoma mai kyau ba.
Allah shi kyauta gaba.
©Rariya

