Wasu rahotanni daga jihar Kano sun bayyana cewa aƙalla mutane 17 ne su ka jikkata, bayan da wasu fusatattun matasa su ka kaiwa tawagar yaƙin neman zaɓen ɗan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC, Abdussalam Abdulkarim Zaura. AA Zaura
Bayan an sun cigaba da cewa matasan sun lalata motoci goma sha bakwai da su ke cikin tawagar ta Abdussalam Zaura kamar yadda Ibrahim Mu’azzam mai magana da yawunsa ya tabbatarwa da manema labarai.
Ibrahim Mu’azzam ya ce lamarin ya faru ne ranar Asabar a lokacin da tawagar ɗan takarar Sanatan Kano ta tsakiyan ta ke wucewa ta ƙauyen Gayawa da ke yankin ƙaramar hukumar Ungogo.
Tuni dai babban daraktan yaƙin neman zaɓen Abdussalam Zaura ɗin, Yahaya Adamu Garun Ali ya bayyana cewa sun rubuta korafin faruwar abin ga kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano domin daukar matakin da ya dace.

