Haramin daya cikin jikokin Manzon Allah (A.S), ya bada kyaututtuka da kudade ga mutanen da suke fama da nakasar barin jiki


 A ranar Lahadi, 04 ga watan Disamba ne, Haramin jikan Manzon (S), dake Birnin Mashhad a kasar Iran, inda ranar ta yi daida da ranar da ake tunawa da nakasassu na duniya, Haramin ya kai ziyara gidan wasu nakasassu tare da yi musu goma ta arziki.


Haramin Ali ibn Musa al-Rida, wanda kuma aka fi sani da Abū al-Hasan al-Thāni, wanda ya ke daya ne cikin zuriyar annabin musulunci Muhammad (S.A.W), wanda mabiya Shi'a ke itiqadin shine Imami na takwas a cikin limamai goma sha biyu wanda ya gaji mahaifinsa, Musa al-Kazim, Kuma yana daga cikin jerin hukunce-hukuncen sufanci a cikin darikun Sufaye na Shi'a biyayya gare su.


Kamar yadda shafin Haramin ya wallafa a kafar Tuwita, sun tawaito cewa; "Yayin da ake gudanar da bukukuwan ranar nakasassu ta duniya, bayin (masu hidima) a haramain Imam Riza (as) sun kai ziyara ga iyalai da nakasassu 3 da ke zaune a birnin Mashhad. Sun yi musu kyauta mai albarka da kuma taimakon kuɗi." Wallafar ta bayyana.


Ga wasu hotuna a kasa 👇👇




Post a Comment

Previous Post Next Post