Wata kungiyar kare hakkin bil'adama ta ce hukumar shari'a ta Saudiyya ta yanke hukuncin kisa ga wasu fursunoni shida kamar yadda masarautar ke amfani da gwaji a asirce da hukunce-hukunce masu kawo cece-kuce a matsayin wani makami na kara murkushe fursunonin siyasa da yiwuwar kawar da su.
Sanad, kungiyar kare hakkin dan adam, wacce ke kare hakkin siyasa da na jama'a a Saudi Arabiya, ta ce an zartar da hukuncin ne ba tare da la’akari da koke-koke da sukar da kasashen duniya suke yi kan aiwatar da hukuncin kisa ba ga ‘yan kasar Saudiyya a hannun gwamnati, Press TV ta labarata.
Sanad ta ce an yanke hukuncin kisa ne a kan Mohammed Al Tahnoon, Mustafa Abu Shaheen, Abdullah Ghazwi, Zuhair Al Samkhan, Mohammed Al Masbah da Razi al-Shayib.
A cewar kungiyar kare hakkin dan adam din, sabon hukuncin kisa na kara fuskantar da yunkurin fille kan ‘yan adawa da ake tsare da su a gidan yari kimanin mutane 59.
Sanad har ila yau, ta jaddada cewa, gwamnatin Saudiyya ta yi watsi da gargadin da kasashen duniya ke yi a wannan fanni, kuma tana ci gaba da zartar da hukuncin kisa ba gaira ba dalili kan abokan hamayyarta na siyasa.
A karshen watan Oktoba, Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta Turai (ESOHR) a cikin wani rahoto da aka fitar na cewa kotunan kasar Saudiyya sun yankewa wasu masu adawa da mulkin kama karya hukuncin kisa biyo bayan shari'ar rashin adalci kuma bisa ikirari da aka samu ta hanyar azabtarwa da musgunawa.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa ta ce mahukuntan Saudiyya sun zartar da hukuncin kisa kan wasu karin fursunoni 15.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun yi zargin cewa, hukuncin da kotun kasar Saudiyya ta yanke wa 'yan adawa da ke zaman gidan yari na nuni da irin yadda masarautar ta yi watsi da dokokin kasa da kasa, wanda hakan bai zama bakon abilu ba a kasar, ta yadda suke yanke hukunci da take hakki da yancin jama'a.
Tun bayan da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya zama shugaban kasar Saudiyya a shekarar 2017, masarautar ta kama daruruwan masu fafutuka, masu rubutun ra’ayin yanar gizo, ’yan boko da sauran su saboda fafutukarsu ta siyasa, da ke nuna kusan ba za su iya jure wa ‘yan adawa ba ko da a cikin la’akarin da kasashen duniya suke yi na murkushe wannan mataki.
Saudiyya ta tsare matar da da wata diyar ‘yar adawar kasar da aka daure a gidan yari yayin da ake ci gaba da murkushe masu zanga-zanga, yayin da a gefe guda an kashe Malaman musulmi kana kuma an saka masu fafutukar kare hakkin mata a gidan yari tare da azabtar da su yayin da hukumomin masarautar ke ci gaba da hana 'yancin fadin albarkacin baki, da dakile sauran kungiyoyi da sauransu.
A cikin shekarun da suka gabata, Riyadh ta kuma sake fasalin dokokinta na yaki da ta'addanci da nufin kai hare-hare kan masu rajin kare hakkin bil'adama.
