Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kai samame a kan shahararran Gidan wasan Ali jita in da tayi nasarar dakile auren jinsi tsakanin wasu yan daudu biyu,
Babban kwamandan Hisbah sheiek Haroon Muhammad Sani Ibn Sina yace yan daudu masu suna Mujahid da Abba sunyi nasarar tserewa amma an kama uwar dakinsu wacce ta shirya bikin ranar haihuwarta Mai suna Salma Fulani,
Ibn Sina yace sunyi nasarar kamo yammata goma sha tara, yayin da mazan da suke wurin suka tsere amma anyi nasarar kama mai kula da gidan shirya bikin.
Babban kwamandan hukumar yace abin takaicin shi ne yadda yammatan suke da kananun shekaru amma sun bujirewa koyarwar manzon Allah SAW da iyayensu har suke aikata mummunan son zuciyarsu irin wannan,
Ya kuma bayyana cewar za su gayyaci iyayen yaran da suke da hannu a yanzu haka domin ja musu kunne.
Hakazalika ya ce, mafi yawan yammatan ba haifaffun jihar Kano bane sun zo ne daga mabambantan jihohi, don haka yayi kira ga iyayen da su rinka kokarin sanin abokan mu'amalar 'ya’yan su don kaucewa haduwarsu da bata gari.

