Babba Bankin CBN ya fitar da samubar Sanarwar Akan gayyade adadin kudin da kowa zai cire a banki a kowacce Rana.
A Rahotan daya shigo mana yanzu haka Babban Bankin Nijeriya CBN ya kara adadin kudaden da ’Yan Najeriya za su Iya cirewa duk mako daya, daga dubu 100,000 zuwa dubu 500,000.
Babban Bankin na Najeriya ya kara adadin tsabar kudi da 'yan Najeriya za su iya cirewa a Asusun banki duk mako zuwa N500,000, yayin da kamfanoni za su iya cire Naira miliyan 5 duk mako.
Wannan karin na zuwa ne a cikin wata wasika da CBN ya aikewa dukkan bankunan kasar nan a ranar Laraba 21 ga watan Disamba, The Cable ta ruwaito. Cewa Babban bankin ya yanke wannan shawarar ne bayan sauraran korafe-korafe daga masu ruwa da tsaki a Najeriya.
