Idan Peter Obi Baici Zaɓe Ba Zamu Tattara Kayanmu Mu Koma Kamaru - Babachir Lawal


 

RAHOTO daga Comrd Yusha'u Garba Shanga.

2023 Bansan me jam'iyyar APC ke jira gareni da haryzanzu basu koreni ba


Tsohon sakataren gwamnatin tarayya kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulki, Engr. Babachir Lawal, ya ce shi Peter Obi na jam’iyyar Labour ne zaɓinshi, inda ya bayyana mamakinsa cewa na rashin korarsa da Jam'iyyar APC ba (Lawal).


Ya ƙara da cewa zaben shugaban kasa na 2023 ya zama dole ga Peter Obi, idan aka yi la’akari da halin da kasar nan ke ciki.


Lawal ya bayyana haka ne a ranar Litinin ɗin da ta gabata a wani taron tattaunawa tsakanin Obi da masu ruwa da tsaki na yanƙin arewa maso gabas a Abuja.


Kalaman Lawal: “Ni ɗan APC ne kuma memba ne a kwamitin amintattu na jam’iyyar, amma ina yin tafiyar Peter Obi/Yusuf Datti.


“APC ba ta kore ni ba har yanzu. Ban san abin da suke jira ba.


“Muna son (Obi) ya ci zaɓen nan kuma dole ne ya ci wannan zaɓen. Idan muka faɗi wannan zaɓe, dukkanmu za mu yi hijira zuwa Kamaru saboda kunya da rashin cin nasara. Ba batun ko muna da zaɓi ba, dole ne Peter Obi ya lashe wannan zaɓe.


“’Yan Najeriya na kishin kawo sauyi kuma mutane sun kuduri aniyar cewa a wannan karon canjin da muke fata zai zo.


“An yi sa’a, muna da ƙwararren mutum a cikin Peter da abokin takararsa. Muna buƙatar kan kibiya don fitar da wannan canjin kuma waɗannan biyun sun samar da shi.


“Ba na sha’awar LP a matsayin jam’iyya. Ina sha'awar Peter Obi a matsayin dan takarar shugaban kasa. Ba ruwan jam’iyyar Peter Obi, ina ganin ‘yan Najeriya sun cancanci a samu canji.


“Sun dade suna neman sauyi; Ra’ayina shi ne Najeriya za ta zabi kowa muddin ba ya cikin PDP ko APC.”


Mai Tawagar, Engr. Isaac Balami ya bayyana cewa taron tattaunawa na da nufin nemo hanyoyin tunzura jama'a don tattara su Obi/Datti da kuma tabbatar da nasarar su ta zo ranar 25 ga Fabrairu, 2023.


"Taron mu a nan shi ne ganawa kan yadda za mu tabbatar da nasara ga Obi/Datti," in ji shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post