Na Yi Kokarina ga 'yan Nigeria A Matsayina Na Shugaban ƙasa – Buhari
Muhammadu Buhari ya ce ya yi iyakacin ƙoƙarinsa ga Najeriya a matsayinsa na shugaban ƙasa.
Buhari ya bayyana haka ne a birnin Washington yayin da yake karɓar babban sakataren dandalin Abu Dhabi, Sheikh Al-Mahfoudh Bin Bayyah da mataimakinsa Fasto Bob Roberts na Amurka da suka kawo masa ziyara.
A cikin sanarwar da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar, shugaban ya bayyana cewa magance matsalolin da suka addabi matasa shi ne abin da gwamnatinsa ta sa a gaba domin su ne alƙawarin da ta ɗauka na samar da makoma mai kyau agaresu.
Buhari ya kuma bayyana buƙatar tada matasan da ba su da tsattsauran ra'ayi dakuma son zuciya.
Yace;
"Muna da girma da yawan jama'a, muna fuskantar ƙalubale da yawa, amma a wurare da yawa, muna ƙoƙari matuƙa. A cikin shekaru bakwai da rabi, na yi iya ƙoƙarina.
“Ayyukan ku na da matuƙar muhimmanci wajen taimakawa, musamman matasa, su fahimci juna, a lokaci guda, su yi alfahari da abubuwan da suka gada.
“Wannan babban shiri da ku zai taimaka wa tsararraki masu zuwa don yin shiri mai kyau da zama tare cikin lumana. A ɓangarenmu, za mu ci gaba da magance matsalolinmu, musamman yadda suka shafi matasa.”
RAHOTO:- COMRD YUSHA'U GARBA SHANGA.
Tags:
DANDALIN SIYASAR NIGERIA
