Uwar gida ta maka mijinta a kotu dake Abuja saboda ya auri mata biyu a asirce.

Uwar gida ta maka mijinta a kotu dake Abuja saboda ya auri mata biyu a asirce.


Ta maka Mijinta a Kuto Sabida ya Auri Wasu Mata Biyu a Asirce ba ta da masaniya.
 

Wata matar aure mai suna Amina Muhammad ta maka mijinta Salisu Mohammed a gaban wata kotun gargajiya da ke Nyanya, Abuja, bisa zargin yin auren sirri da wasu mata biyu.


Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ta ruwaito, mai shigar da kara dake zaune a unguwar Mararaba, Abuja, babban birnin tarayya Abuja, ta yi wannan zargin ne a wata takardar sakin da ta kai kan mijinta.


Ta yi zargin cewa mijinta ya auri wasu mata biyu a asirce kuma ya yi musu hayar gidaje a wurare daban-daban a Abuja, yayin da suka tafi suka barta a Mararaba.


Amina ta bayyana cewa mijin nata ya sha yi mata barazanar cewa zai sake ta tare da kore ta da karfi daga gidan aurenta.


 Ta kara da cewa wanda ake zargin ya shafe sama da shekaru biyar basuyi kwanciyar aure ba. 


Rahoto:Kamal Aliyu Sabongida

Post a Comment

Previous Post Next Post