Kocin kasar Brazil, Adenor Leonardo Bacchi da aka sani da Tite, ya ajiye aikinsa na horar da tawagar ’yan wasan kasar bayan rashin zuwa matakin kusa da na Karshe a Gasar Kofin duniya da ke gudana a kasar Qatar.
Tite Mai shekaru 61, ya ajiye aikinsa ne jim kadan bayan Crotia ta doke Brazil a bugun fanareti a wasan Kwata-Fainal da suka buga a yammacin jiya Juma’a.
Kasar Crocatia dai ta fitar da Japan a zagayen ’Yan 16 a bugun fanareti, sannan ta maimaita irin wannan nasara a karawarta da Brazil a yammacin ranar Juma’a.
A shekarar 2016 ne dai Tite ya karbi Jagorancin ragamar horar da tawagar ’yan wasan, inda ya jagorance ta wajen lashe Gasar Copa America a shekarar 2019.
Tags:
DANDALIN WASANNI

