YANZU YANZU; Sheikh Hamza Lawal Badikko Kaduna ya rasu.


Rahotanni daga bJaridar HASKEN SHIRIYA sun bayyana cewa Shehin Malamin nan na addinin Musulunci dake zaune a Kaduna, Shaikh Hamza Muhammad Lawal Badikko ya rasu.

Bayanai daga makusantan Shehin Malamin sun tabbatar da labarin rasuwar Malamin. Sai dai ba su fayyace ma majiyarmu yadda Shehin Malamin ya rasu ba kuma yaushe ba.

Ya zuwa hada takaitaccen rahoton nan, babu wata sanarwa a hukumance daga iyalan mamacin ko makusantansa kan rasuwarsa.

kafun rasuwar sa shine Shugaban ƙungiyar Thakalayn Foundation a Nigeria,

TUSHE HASKEN SHIRIYA

Post a Comment

Previous Post Next Post