Malamin Addini Yana Iya Shiga Siyasa A Dama Da Shi, Amma Da Sharadin...— Sheikh Maqari

Dakta Ibrahim Maqari
Hoto: sheikhmaqari.com.ng

 Shahararren Malamin addini Muslunci, kuma limamin babban Masallacin kasa dake Abuja, Sheikh Ibrahim Maqari ne ya fadi hakan.

Shahin malamin a wata wallafa data fito daga shafinsa na Tuwita, ya bayyana cewa; "Malami yana da cikakkiyar 'yancin ya shiga siyasa shi kadai...".

Ya kuma kara yana kai kawo batun cewa; " Amma zai zama ci da addini idan har yayi amfani da yawan mabiyansa wajen samun karbuwa gun 'yan siyasa." inji shi.

Malam ya nuna cewa, shiga siyasa ba matsala bane, amma amfani da mutanen dake ƙarƙashin ka suka yi imani da kai ko mabiyan dake tare da kai a harkar addini, to yin hakan ci da addini ne.

Furucin nasa na zuwa ne lokacin da mutane ke ta martani kan wani bayani da Sheikh Kabiru Gombe ya yi na koda mahaifiyar dan takarar shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Ga yadda wallafar tasa ta zo a Tuwitar 👇👇


Post a Comment

Previous Post Next Post