Za'a ƙarawa manyan ƴan Sandan Nigeria 745 girma zuwa muƙami na gaba.

Za'a ƙarawa manyan ƴan Sandan Nigeria 745 girma zuwa muƙami na gaba.
Nigeria Police 

Hukumar kula da ‘yan sanda ta ƙasa (PSC) ta amince da ƙarin girma ga manyan jami’an ‘yan sanda 745 zuwa muƙami na gaba bayan an tantance su.

Hukumar ta PSC ta kuma yi nazari tare da amincewa da sanyawa kwamishinonin ‘yan sanda biyar da mataimakin ƙwamishinan ‘yan sanda yadda ya kamata, kamar yadda ta kuma bibiyi ƙararraki 14 da ƙorafe-ƙorafe da kuma wasu batutuwan ladabtarwa guda tara da ke jiran korar jami’an ‘yan sanda da aka kora.

Kakakin hukumar ta PSC, Ikechukwu Ani, ya ce sun yanke shawarar wasu daga cikin muhimman batutuwan da aka gudanar a babban taron hukumar karo na 18, wanda aka kammala a Abuja ranar Talata, 13 ga watan Disamba, 2022 wanda shugaban riko na hukumar, Justice Clara Bata Ogunbiyi ya jagoranta.

Ya kuma ce hukumar ta PSC ta kuma ƙarawa wasu mataimakan Sufiritandandan ‘yan sanda biyu (DSP) ƙarin girma zuwa Sufiritandan ‘yan sanda, mataimakan Sufurtandan ‘yan sanda 696 zuwa mataimakan Sufurtandan ‘yan sanda da kuma Sufeto ‘yan sanda 47 zuwa mataimakan Sufiritanda (ASP11) da ba a tabbatar da su ba.

Sabbin Sufetodan ‘yan sandan da aka samu ƙarin girma sun haɗa da: Yusuf Bello da Titus Ogboku Obaji yayin da wasu daga cikin mataimakan sufiritandan ‘yan sanda 696 da aka ƙara wa girma, sun haɗa da Ogbu Emmanuel Nwachukwu, kwamandan jihar Abia, Haruna Hotoro, rundunar jihar Ekiti, Ogbe Anthonia, reshen jihar Filato; Sadisu Oyarekhua, FCID, ya hade Legas da Bala Dambu, jihar Kebbi.

Daga cikin sufeto 47 da aka yiwa ƙarin girma zuwa mataimakan Sufeto Janar na ‘yan sanda, ASP11, 44 sun fito ne daga hedikwatar ‘yan sanda ta shiyyar 9 a Umuahia, jihar Abia.

Sun haɗa da Daniel Maiwada, Paul Aguwa, Oruma James, Momoh Mohammed, Hosea John, Danjuma Likita, Omale Nathaniel, John Ononaku, Ogbonnaya Ugochukwu da Ikpo Kalu. Sauran su ne; Oju Ismaila, Ngozika Christopher, Obinna Anyanwu, Iheamachanma Nkechi, Ungbo Moses, Abuh James, Kyaaja Peter, Bakari Edward, Haruna Ayuba, Aliyu Mohammed da Auta Akila.

Hukumar ta amince da sanyawa da kuma daidaita kwanakin ƙarin girma na CP Njoku Henry Eronini, CP Afolabi Babatola Adeniyi da CP Taiwo Olusola Jesubiyi a cikin jerin sunayen ma’aikatan CP daga ranar 24 ga Maris, 2022 zuwa 09 ga Maris, 2022 domin samun ci gaba a rundunar.

Hakanan ta daidaita ranar girmar CP Ogundele Ayodeji zuwa 3 ga Yuni, 2021 maimakon 9 ga Maris, 2022.

Hukumar ta kuma daidaita ranar tabbatar da DCP Nwonyi Polycap Emeka zuwa ranar 7 ga Disamba, 2018 maimakon 9 ga Satumba, 2020.

Hukumar ta amince da rage ma’aikatan ‘yan sanda huɗu muƙami tare da hukunta wasu shida na tsawatarwa.

Ta mayar da jami’ai 6 aiki, biyu sun yi ritaya saboda amfanin jama’a, sannan ta ƙara wa daya DCP Emmanuel Eze ƙarin girma zuwa CP sannan ta yi masa ritaya.

Ta yi nazari kan hukuncin rage masa mukamin Sufeto Falade Kayode, inda ta wanke shi tare da mayar masa da matsayin ASP 1.

Post a Comment

Previous Post Next Post