Ana zargin wasu jami’an ƴan sanda guda biyu a jihar Kano da ke a arewacin Najeriya da harbe wani matashi mai kimanin shekaru 35 kwana ɗaya bayan wata taƙaddama ta faru a tsakaninsu.
Matashin mai suna Mukhtar Bala mazaunin unguwar Kwalli da ke yankin karamar hukumar Birnin Kano ya hadu da ajalinsa ne kwana ɗaya da yin sa -in -sa da wasu jami’an ƴan sanda Holanda da Gaddafi kamar yadda dan uwan mamacin Yakubu Babangida ya tabbatarwa manema labarai,
Yakubu Babangida ya kara da cewa a lokacin taƙadammar an jiyo Holanda yana ikirarin sai ya hallaka Mukhtar Bala.
“Holanda ya bayyana cewa wallahi sai ya kashe Mukhtar Bala a lokacin da su ka taƙaddama”
Lamarin dai ya faru ne a kusa da ofishin ‘yan sanda na Kwalli a daren jiya juma’a, abinda kuma ya harzuka iyalan mamacin.
A lokacin haɗa wannan rahoton babu wata sanarwa daga hukumar ƴan sanda ta jihar Kano akan batun.
Ba wannan ne karon farko da ake samun jami’an da hallaka mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, domin ko a shekarar 2020 sai da aka zargi wasu jami’an ƴan sanda da kisan wasu matasa guda biyu a yankin unguwar Sharada a birnin na Kano.
Babu ko ko shakka zargin kisan azarɓaɓi, da cin zarafi da kuma wuce gona da irin da ake yi wa ƴan sanda a Najeriya, abu ne da ya zama ruwan dare sai dai ukumomin ƴan sanda kan cewa su na ladabtar da wadanda ke aikata kisan tare da sallamarsu daga aiki, sai dai hakan ba ya hana sake afkuwar lamarin.
