Buhari Ya Jajantawa Waɗanda Haɗarin Kwalekwalen Ruwa Faɗawa Na Jihar Kebbi

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Kebbi kan asarar rayuka da dama, biyo bayan kifewar wani jirgin ruwa da ke jigilar manoma ya afku.

Shugaba Buhari a cikin wata sanarwa ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Femi Adesina, a ranar Juma’a, ya jajanta wa iyalan da suka rasa ‘yan uwansu a hatsarin, inda ya buƙaci a kara yin addu’a ga wadanda aka ceto da ake ci gaba da duba lafiyarsu.

Shugaban ya yaba da ƙoƙarin ma’aikatan ceto, waɗanda suka kwashe kwanaki suna aikin neman waɗanda suka ɓata, yayin da ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su mai da hankali kan yadda ya kamata wajen tafiyar da zirga-zirgar jiragen ruwa, musamman a yankunan karkara.

Haka zalika shugaba Buhari ya yi addu’ar Allah ya karbi rayukan waɗanda suka rasu.

RAHOTO DAGA:- Comrade Yusha'u Garba Shanga.

Post a Comment

Previous Post Next Post