Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta kama wani Issa Naigheti da laifin yin garkuwa da mahaifinsa tare da karɓar kuɗin fansa N2.5m. miliyan biyu da rabi.
Ajayi Okasanmi, kakakin rundunar, wanda ya bayyana hakan, ya ce an kama wanda ake zargin ne a kusa da unguwar Kambi agarin Ilorin.
Ya ce jami’an rundunar da ke yaƙi da garkuwa da mutane na rundunar ‘yan sandan jihar Kwara sun cafke wanda ake zargin ne a yayin da ake bin sawun waɗanda ake zargin masu garkuwa da mutane.
Acikin rahoton Okasanmi ya ƙara da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin kamo sauran waɗanda ke da hannu shuni a cikin lamarin.
“Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da cewa ya haɗa baki da wasu mutane biyu don sace mahaifinsa, Bature Naigboho a yankin Igboho/Igbeti a jihar Oyo kuma ya karbi kudin fansa N2.5m,” in ji Okasanmi.
Ya kara da cewa za a mika karar zuwa jihar Oyo, inda aka aikata laifin.
RAHOTO DAGA:- Comrade Yusha'u Garba Shanga.
