An kama Daraktan Otal da zargin harbin wani da bindiga lokacin da suke jayayya kan kuɗin ɗaki.
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wani Kingsley Enageghe, daraktan otal da ke unguwar Surulere a jihar bisa zargin harbin bindiga a wani bako a otal ɗin, a ranar Alhamis 5 ga watan Janairu.
A cewar rahoton LIB, Engageghe ya gayyaci ma’aikatansa ne domin su ba da bayanin wani ɗaki da kwastomominsa ke ciki. An ce ma’aikatan sun shaida wa Enageghe cewa baƙon ya biya kuɗin kwanakin da ya sauka a baya.
"Daraktan ya dage cewa dole ne baƙon ya biya kuɗin ranar amma baƙon ya ƙi. An yi ta cece-kuce bayan da Mr.Enageghe ya shiga ofishinsa, ya fito da bindigar ganga guda, sannan ya yi harbin kan baƙon da ƙafafu, lamarin da ya jawo musu rauni a jiki.
Ma’aikatan da suka jikkata sun kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda na sashen kuma nan take aka cafke wanda ake zargin yayin da aka ƙwato bindigar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga LIB, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya ce;
"An kama wanda ake zargin kuma za a gurfanar da shi gaban kotu da zarar an kammala bincike".
RAHOTO DAGA:- Comrade Yusha'u Garba Shanga.

