Al'umma na cigaba da fuskantar matsaloli ta fuskar karancin sabbin kudade a Jihar Kano,
A zagayen da Wakilinmu ya yi a wasu ungunnin na cikin birnin Kano da yammacin jiya Juma'a da yau Asabar ya nuna cewa har yanzu akwai dogayen layukan jama'a a wajen cire kuɗi.
Wannan dai na zuwa ne dai a daidai lokacin da masana ke ta kiraye-kiraye kara wa'adin karɓar kudin domin samun sauƙi rayuwa.
