Fitaccen jarumi a masana'antar Kannywood Shamsu Dan'iya ya samu haɗari mota a kan hanyarsa ta Zariya zuwa Kano.
Cikin sakon sautin murya da ya aikawa Wakilin Inuwar labarai, Shamsu ya ce bai yi rauni ba ko kwallo ba, amma motar ta yi kaca-kaca.
Hakazalika, ya cigaba da cewa " A kan hanyar dawowa ta daga Zariya a daidai karamar hukumar Kura sai tayar gabar motar ta fashe, nan take motar ta dinga juyawa Allah ya taimakeni ta tsaya na samu na fita".
Bugu da kari; kuma cikin ikon Allah ba a fi minti ɗaya da samun haɗarin ba sai ga Umar M. Sharif ya zo wucewa har ya wuce sai ya tsaya" in ji Shamsu Dan'iya.
