Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IGP), Usman Baba, ya yi kira ga iyaye da su ƙarfafa ‘ya’yansu don yin aikin ‘yan sanda a ƙasar nan.
A cewar IGP, rundunar ‘yan sandan Najeriya na ɗaya daga cikin hanyoyin da ake dogaro da su wajen ciyar da ƙasa, tare da wasu hidindimu na rayuwa.
IGP ya bayyana hakan ne a yayin bikin zagayowar sabbin ‘yan sanda 374 da aka ɗauka a kwalejin horas da ‘yan sanda da ke Oyin-Akoko, ƙaramar hukumar mulki ta Akoko, Arewa maso Yamma ta jihar Ondo.
IGP, wanda ya samu wakilcin mataimakin babban sufeton ‘yan sanda mai kula da shiyya ta 17 a Akure, Yunus Akeera, ya jadadda cewa ganin yadda matasa ke sha’awar aikin ‘yan sandan ƙasar nan, ko shakka babu zai ɗore da hangen nesa dazai samar da ingantaccen tsarin acikin aikin ‘yan sanda. .
Yayin da yake jaddada cewa rundunar ‘yan sandan ba ta da wani haƙƙi na rashin ɗa’a, ya shawarci sabbin ‘yan sandan tare da gargaɗi akan kada su shiga ayyukan da za su iya ɓata sunayensu, kokuma wata mummunar ɗabi'a zata kasan ce masu sana’ar yi.
Akeera ya ƙara da cewa za a tura sabbin jami’an ‘yan sandan ne domin su ƙarawa jami’an da ke aikin zaɓe ƙwarin gwiwa a shekarar 2023.
Ya yaba da yadda shugaban ƙasa Mohammadu Buhari ya jajirce wajen mayar da rundunar ‘yan sandan Najeriya matsayin tambarin zamani.
A nasa jawabin, kwamandan kwalejin horas da ‘yan sanda, Oyin-Akoko da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Adebayo Rafiu, waɗanda suka taya ‘yan sandan murna, sun buƙaci su kasance masu nuna rashin son kai da kishin ƙasa yayin gudanar da ayyukansu.
Ya ce: “Ina kuma rokon ku da ku ci gaba da sabunta ilimin da kuka samu ta hanyar sanya duk abin da kuka koya a aikace a fagen ɗaukaka matakin da ya dace da kuma kwarewa wajen gudanar da ayyukanku na doka.
RAHOTO:- COMRD YUSHA'U GARBA SHANGA.
