ABUN AL-AJABI:Wani Uba ya canzawa Ɗiyar sa Suna a Jihar Katsina....

Wani mahaifin yarinya Mai suna Yahuza Ibrahim Niga dake cikin ƙaramar hukumar mulki ta JIBIA dake jihar Katsina ya chanzama ɗiyar shi suna daga "Buhariyya" zuwa "Kausar"

Da aka tambaye shi minene dalilin shi nayin hakan sai yace sanadiyyar Rashin cika Alƙawarin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da Jam'iyyar APC sukayi a yayin da suke neman ƙuri'un Jama'a a Shekarar Dubu Biyu da Goma Sha Biyar.

Shi dai wannan bawan Allah kamar yadda yajadda wa manema labarai cewa shi Masoyin Shugaba Buhari ne na haƙiƙa, kuma duk wanda yaji sunan Buhari yasan Mutum ne mai gaskiya, amma dai yanzu ya dawo rakiyar shi.
"Yace tun a shekarar 2015 lokacin Buhari yana sauran kwana 26 yashiga office matarshi na gab da zata haihu, yayi Alƙawarin cewa idan Allah ya sauketa lafiya zai sakama Ɗan suna Buhari, haka zalika Kuma idan macece zai saka mata suna Buhariyya sai akasamu mace acikin iyawar ALLAH.

"Akasin ba namiji bane yasakamata wannan sunan amman yanzu ya chanzamata shi, bisa dalilai na rashin cika Alƙawari.
Haka Kuma mahaifin yarinyar yace ya jinkirta sanya Yarinyar Makarantar Primary ne saboda yanaso zai chanzamata suna kafin ta fara zuwa karatu.

RAHOTO:- COMRADE YUSHA'U GARBA SHANGA.

Post a Comment

Previous Post Next Post