Masu kungiyoyin PSG sun shirya sayen Tottenham domin kalubalantar Manchester City.



Mamallakan kungiyar Kwallon kafa Paris Saint-Germain suna so su kafa wata hamshakiyar kungiya a wajen Faransa. Qatar Sport Investment (QSI), wanda su ne mamallaka PSG, suna neman siyan Tottenham.


'CBS Sports' ta rahoto cewa Yan kasar Qatar QSI da shugaban PSG Nasser Al-Khelaïfi sun riga sun yi ganawar farko tsakanin su mai kungiyar Tottenham Daniel Levy.



Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da QSI ke sha'awar siyan kungiya daga Ingila ba. 


Ko a baya-bayan ma sun nemi sayen Leeds United sai dai kungiyar ta riga ta yi watsi da tayin na su kuma yanzu sun tafi domin sayen Tottenham.

Post a Comment

Previous Post Next Post