Assalamu Alaikum jama'a barkanmu da wannan lokaci sannunku da sake kasancewa damu a wannan shafi namu mai Albarka.
A yau nazo muku da wani bayani akan sabuwar hanyar da yan damfara suke amfani da ita wajen satar muku kudi ko kuma a wani abun a waya ba tare da kun danna Link ko cika wani form na su ba.
BA DOLE SAIKA CIKE WANI TSARI KO FORM AKE SATAR MAKA KUDI BA.....
Akwai wani tsari da yan damfara suka fito da shi a kwanan nan, kamar yanda muka sani akwai wani Virus da hakas suke amfani dashi mai suna (trojan virus) wanda yake bawa mai shi damar sarrafa waya ko computer ka ba tare da saninka ba, sai dai shi wannan trojan din dole sai da yardar ka kafin ya zauna acikin wayarka ko computerka shi yasa wasu lokutan hackers sun fi amfani da ababen yau da kullum kafin su sami damar yi maka kutse, misali a wasu lokutan a wayar ka zaka rika ganin vidoes ko photo na batsa wanda kai bakasan ya akayi ka gansu ba a saman wall din wayarka to idan kace zaka kalla kana danna link din shikenan ka baiwa (trojan virus) damar zama cikin wayarka, wasu kuma tallan littafi wasu agogo, kowa dai da yanda suke bibiyar wayarshi suga me yafi so.
To yanzu sun daina amfani da trojan virus wani sako ne za a turo maka sako da unknown number kamar yadda kuka gani a message dina, da zaran ka bude sakon kuma har ka danna download shikenan ka baiwa virus din damar zama a wayarka, kuma zasu na amfani da wayarka su kwashe maka sirrin bankin ka da kudadenka, haka kuma su hackers da scammers kullun cikin bincike da salon hanyar zaluntar al'umma suke, bai zama wannan ce kadai hanyarda suke amfani da ita ba, dan haka sai mun kiyaye, kubar shiga kowanne irin link da sunan wai wani dan takara zai bada kudi, indai ba kun aminta da link din bane.
©Bin Muhd Alpotiskumi
Tags:
DAMFARA
