Wani rahoto dake yawo a kafafen sada zumunta sun bayyana hoton shahararren dan kwallon Portugal, Cristiano Ronaldo a gaban Ka'aba da Hirami, yayin da ake cewa; "Ronaldo ya musulunta".
Saidai rahoto daga majiyar Inuwar Labarai, wanda shafin Kamfanin Ƙwallon kafar Saudiyya, Al-Nasr suka fitar ya ƙaryata lamarin.
Al-Nasr ta ce kwanaki biyu da suka gabata ne suka kulla yarjejeniya da tauraron dan kasar Portugal na buga kwallo a kulob dinsa na tsawon kaka biyu da rabi.
In ba a manta ba, a cikin satin daya gabata ne Saudiyya ta nawa Dan kwallon damar ci gaba da zaman dadiro da Budurwarsa, Georgina Rodriguez a kasa mai tsarki, har tsawon kammala kwantiraginsu da shi.
Har yanzu Ronaldo bai fara buga wasa da Al-Nusra ba
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya nakalto majiyar ta ce duk da katin da Ronaldo ta ba shi na kasa da kasa domin buga wasa a Al-Nasr, ba zai iya buga wa kungiyar wasa ba, saboda an yanke masa hukuncin dakatar da shi a Manchester United.
Hukuncin da aka yankewa É—an wasan ya biyo bayan fasa wayar da ya yi na daya daga cikin masoyansa.

