![]() |
| Sheikh Abduljabbar |
Malam Abduljabbar Shaikh Nasir Kabara wanda Kotu ta zartarwa da hukuncin kisa ta hanyar rataya ya ce bai gamsu da hukuncin da aka yi masa ba gaba daya.
Wannan na kunshe ne cikin wata takarda da lauyansa ya mikawa babbar kotun jihar Kano. Takarda inda ya ke cewa:
"Ni Abduljabbar ban gamsu da hukuncin da Kotun Shari’ar Musulunci ta Kofar Kudu ta yanke a kaina ba, a shari’a mai lamba CR/01/2021 da aka zartar ranar 15th December, 2022, Ć™arĆ™ashin Alkali Ibrahim Sarki Yola.
Abduljabbar ya daukaka kara zuwa babbar kotun jihar kano bisa dalilin da ya bayyana a sakin layi na 3 na takardar daukaka ƙarar.
Cikin takardar yace bai yarda da dukkan hukuncin da karamar kotun ta yanke masa ba.
Ya kuma bukaci kotun daukaka kara da ta yi la’akari da duk bukatun da ya bayyana a sakin layi na 4 na wannan takardan daukaka kara.
Malam Abduljabbar din ya cigaba da bayyana cewa ya bayyana sunayen duk wadanda wannan roko ya shafa kai tsaye a sakin layi na 5 na takardan daukaka kara.
Kazalika ya bayyana cewa hukuncin da aka yi masa ya saÉ“a da tanadin da dokar Shari’a ta shekara ta 2000 ta jihar Kano tayi.
Ita dai kotun shari’ar Muslunci dake kofar kudu ta baiwa mal. Abduljabbar da gwamnatin Kano kwanaki 30 daga 15/12/22 domin daukaka kara ga wanda bai gamsu da hukuncin nata ba.
