Daga Ibrahim Hamisu
Ɗan takarar shugabancin ƙasa ƙarƙashin Jam’iyyar (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa gogaggun ‘yan jarida biyu hadimansa domin ƙarfafa ofishinsa na yaɗa labarai.
Waɗanda aka naɗa ɗin su ne; Mahmud Jega a matsayin Mai ba da Shawara na Musamman Kan Sha’anin Hulɗa da Jama’a, sai Abdulaziz Abdulaziz, Hadimi na Musammam Kan Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a.
Kafin naɗin nasa, Jega mai fashin baƙi ne a tashar Arise TV, kuma marubuci a jaridar Thisday, ya kuma riƙe muƙamin Babban Edita na jaridar intanet ta 21st Century Chronicle.
Shi kuwa Abdulaziz, zaƙaƙurin ɗan jarida ne wanda har lambar yabo ya samu, sannan ya taɓa riƙe muƙamin Mataimakin Babban Edita a kamfanin jaridun Daily Trust.
Sanarwar da ofishin yaɗa labarai na Tinubu ya fitar a ƙarshen mako mai ɗauke da hannun Mr. Tunde Rahman, ta ce su biyun za su yi amfani da ƙwarewarsu kan harkokin siyasar ƙasar nan musamman kuma a yankin Arewa, wajen ciyar da tawagar gaba.
Daga cikin wuraren da Jega ya yi aiki har da Jami’ar Usman Danfodio, Sakkwato da kamfani Daily Trust inda ya riƙe matsayin Edita a matakai daban-daban.
Kazalika, ya yi editanJaridun New Nigerian, Editan Mujallar The Sentinel a Kaduna, kana Mataimakin Edita a Mujallar Citizen.
A nasa ɓangaren kuwa, Abdulaziz na da ƙwarewa a ɓangaren jarida da talabijin, kafafen sadarwa na zamani da sauransu.
Sannan ya yi aiki da jaridun LEADERSHIP da Blueprint da kuma Premium Times.

