Rahotanni daga jihar Kano a Arewacin Nijeriya na bayyana cewar, ana zargin Wasu ƴan ƙungiyar Sintirin Bijilante da fasawa wata amarya mai suna Khadija Abdullahi ido ɗaya a unguwar Kwajalawa a birnin Kano.
Majiyar Freedom Radio ta rawaito cewar, Al'amarin ya faru ne a lokacin da amarya da ƙawayenta suke shagali bikinta yayin gudanar da kidan Dj , a nan ne ake zargin wasu daga cikin jami'an bijilantin da far mu su da duka har amarya ma Khadija ta shiga wannan halin, bisa raunata ta a idon.
Amarya Khadija Abdullahi ta kuma zargi ƴan bijilanten da nuna mata bakin ciki ƙarara a lokacin data ke murnar bikin ta ,tare da kira ga mahukunta su kwato mata hakkinta a wajen su.
Mallam Hamisu Bala shi ne Angon Amarya Khadija Abdullahi, shi ma ya bayyana cewa daman yan bijilantin sun yi ikirarin sai sun tarwatsa taron DJn kafin mai afkuwa ta afku.
A cewarsa, “Ina kira ga mahukunta da su bi masa kadi na raunata amaryar ta sa da aka yi a idonta guda ɗaya domin mai unguwar yankin baya so a ɗauki mataki kamar yadda ya nuna, "in ji Ango Hamisu”.
Da yake nasa jawabin Mahaifin Amaryar Mallam Abdu Ma'azu wanda ake kira Baƙo Ɗan kasuwa, ya bayyana takaicinsa da cewa yana Tudun Murtala aka kira shi a waya yayin da aka shaida masa cewar an fasa idon yar tasa, wanda da zuwansa ne ya sanarwa da jami'an ƴan sanda suka haɗu tare suka kaita Asibiti domin nema mata lafiya.
Ita ma Hajiya Amina Abdu, mahaifiyar amarya ta nuna damuwarta akan faruwar lamarin, inda ta ce ranar farin ciki ta zame mu su ta bakin ciki bisa fasawa ƴar tasu ido ranar auren ta.
Rahotanni sun bayyana cewar, yayin da take jawabi Hajara wadda ɗaya ce daga cikin yar uwa ga amaryar da ta rasa idon, ta zargi jami'an bijilantin da kai duka kan mai uwa da wabi, wanda a nan ne wannan al'amari ya faru na gurguntawa amarya idonta guda ɗaya da ta kai ga an rufe shi.
Akan al'amarin ne kuma muka so jin ta bakin ƙungiyar Sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano, sai dai kawo yanzu lamarin ya ci tura, amma zamu ci gaba da tuntuɓa domin matsayar su a kan al'amarin.
