Matar nan da ta fi tsufa a duniya ta mutu tana da shekaru 118 a birnin Toulon da ke yankin yammacin Faransa kamar yadda magajin garin ya sanar a hukumance.
An dai haifi Lucile Randon wacce malamar majami’a ce a ranar 11 ga watan Fabairun shekarar 1904, wato bayan shekaru 10 da kawo karshen yakin duniya na farko, yayin da aka sanya ta a cikin jerin mutane mafiya tsufa a duniya a cikin watan Afrilun bara.
Labarai24, ta ruwaito cewa matar ta yi aiki a matsayin malama mai koyarwa a gida a lokacin da take matashiya, wato gabanin ta mayar da hankali kacokan kan hidimar addini tana tsakan-kanin shekaru 40.
Gabanin mutuwarta, marigayiyar ta yi fama da larurar makanta, sannan ta ci gaba da rayuwa a kan kujerar marasa lafiya.
Ko a shekarar 1944, Randon ta sauya sunanta zuwa Sister Andre, yayin da kundin adana tarihi na duniya, Guiness Book of Record ya bayyana ta a matsayin ta biyu mafi tsufa a cikin al’ummar Faransawa da yankin Turai baki daya da aka taba gani a duniya.
Tags:
DANDALIN TARIHI
