Zargin handame Miliyan 99: Kotu ta daure alkalin kotun Musulunci da mataimakansa a Kano

Kotun Majistare mai lamba 14 ta aike da wani alkali da ma’aikatansa na Hukumar Shari’a gidan gyaran hali saboda zarginsu da wawure Naira miliyan 99.

Mai Shari’a Mustapha Sa’ad Datti ya aike da mutanen ne bisa zargin su da yin sama da fadi da kudaden wasu Marayu.

Hukumar Karbar Korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano ce ta gurfanar da wadanda ake zargin gaban kotun.
Sani Ali, Sani Uba Ali, Bashir Baffa, Gazzali Wada na daga cikin wadanda ake tuhuma, sauran sun hada da Hadi Tijjani Mu’azu, Alkasim Abdullahi tare da Yusuf Abdullahi, Mustafah Bala, da Jaafar Ahmad, Adamu Balarabe, da kuma Aminu Abdulhadi, ragowar sun hada da Abdullahi Sulaiman Zango, Garba Yusuf da Bashir Ali Kurawa tare da Usaina Imam, sune mutanen da suka gurfana a gaban Kotun.

Kunshin karar ta bayyana cewa ana tuhumar alkalan da ma’aikatan kotun shari’ar da laifin hada kai da cin amana da satar Naira miliyan 99.

Wadanda ake zargin duk sun Musanta laifukan bayan karanta musu.

Barista Zaharaddin Kofar Mata shi ne mai gabatar da kara, ya roki kotun da ta sanya wata ranar domin sake gabatar da shaida.

A nasu bangaren lauyoyin wadanda ake kara sun nemi da mai shari’a ya basu beli, amma kotun tayi kememe ta hana bayar da belin nasu.

Daga karshe dai mai shari’a yace a zama na gaba kotu za ta bayyana matsayinta game da rokon belin da aka yi mata, a ranar daya ga watan Fabrairu, 2023 mai zuwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post