Dan Majalisa mai wakilin kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure a majalisar wakilai ta kasa RT Hon Kabiru Alhassan Rurum ya ce ziyara da tawagar Gwamnatin Jam'iyyar APC suka fara ta kwana guda jiya a karamar hukumar Rano babu abinda za ta jawowa Gwamnatin Kano da jam'iyyar APC sai bakin jinin jama'a,
Rurum a ta bakin kakakin sa Fatihu Yusuf Bichi ya jaddada cewa tuni Jama'ar kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure sun daina goyon bayan APC domin taci amanar talaka ba ma na yankin ba na fadin Jihar Kano da kasa ma baki daya,
A cewar Rurum din ko a Shekara Gwamna Ganduje da Dan takarar kujerar Gwamnan na Kano Dr Nasiru Yusuf Gawuna za suyi a garin Rano ba zai sauyawa mutane ra'ayi ba domin dai mutanen yankin sun San abinda su ke a siyasance kuma mutane ne masu goyon bayan akidar da suke kai ta masoyansu na zahiri,
Ya ce kara da cewa "Ina da yakinin al'ummar Kananan hukumominmu Abba Gida Gida da Kawu Sumaila da ni Turakin Rank za ku yi, domin mu cigaba da antayo muku ayyukan raya kasa da cigaban Al'umma" inji Turakin Rano
Tags:
DANDALIN SIYASAR NIGERIA
