DA ƊUMI-DUMI: Daga gobe Juma'a, ba ya halatta ga Bankuna su karɓi tsohon kuɗi

Details from CVN 

Duk tsohon kuɗin da bai samu shiga banki gobe ba sai dai a kai babban bankin Ƙasa CBN kai tsaye, in da za a sauyawa mutum da sabbi.

Kaiwa zuwa CBN da fari deadline ɗin zuwa 17 ga wannan watan na Fabarairu ne. Amma yanzu babu wa'adi. Dan haka daga nan har shekaru aru-aru kana da damar kai tsaffin kuɗaɗenka CBN domin a sauya maka su da sabbi.

Sai dai kuma fa bayan gobe har wa yau, haramun ne a dokar CBN yin cinikayya da tsaffin kuɗaɗen. Dan haka kar ka karɓa, kar kuma ka bayar. Domin idan ka karɓa kai ke da zuwa CBN domin neman sauyi.

Wannan abin da na faɗa yanzu shi ne a dokance. Sai dai babu mamaki zuwa goben wata sanarwar ta tashi wannan hukuncin.

© Na Ƴar Talla

Post a Comment

Previous Post Next Post