Rashin Kuɗi Cash A Hannun Mutane Bai Hana Su Bayar Da Taimako Ga Al’umma Ba– Sheikh Bala Lau

Shugaban ƙungiyar izala ta ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce hakika a wannan azumin ana cikin lokaci mawuyaci na rashin kudi a hannun jama’a wanda sai dai a yi ta godiya ga Allah.

Sheikh Bala Lau ya bayyana haka ne a yayin wata fira da wakilinmu ya yi da shi.

Ya ce, sai dai da ya ke, duk abinda Allah ya sanya shi dole ga bayinsa to kuwa babu shakka zai kawo ma su mafita kan lamarin, don haka ma ne duk da babu kudi a hannun jama’a amma hakan ba yana nufin babu su a asusun ajiya ba.

Sheikh Lau ya ce yanzu ma haka an fi samun taimako daga jama’a fiye da da, tunda dama mafi yawanci ba cash mutane ke dauko kudin su bada ba suna turawa ne ta asusun ajiyarsu.

A karshe ya ce kuma kungiyarsu na nan tana shirye-shiryen rarraba ma mabukata taimakon da aka samu daga jama’a.


Post a Comment

Previous Post Next Post