ABUN AL-AJABI: Yau Sarki Ooni na Ife zai An gwance da mata ta 6.


Ooni na Ife, Oba Enitan Ogunwusi, zai angwance da mata ​​ta shida, Temitope Adesegun, a gobe Litinin, 24 ga Oktoba, 2022.

Jaridar Punch ta rawaito cewa sanarwar ta fito ne daga mai magana da yawun Ooni, Moses Olafare, a cikin wani sakon Facebook da ga wallafa a yau Lahadi.

A ranar Alhamis, 20 ga Oktoba, 2022 me dai Sarkin ya auri matarsa ​​ta biyar kuma wa ce ta kafa dandalin Makon Kwalliya na Afirka, Ronke Ademiluyi wacce ita ce jikanyar Ooni na Ife na 48, Ajagun Ademiluyi.

A cewar Olafare, matar Ooni ta shida mai jiran gado, Adesegun, gimbiya ce wacce ta fito daga yankin Ijebu.

A cikin sakon Facebook, Olafare ya rubuta, “Olori Temitope Adesegun Ogunwusi an Ijebu Princess cum Ile-Ife Queen.

Bayan aurensa da Naomi Silekunola a watan Disamba 2021, sarkin ya auri mata biyar cikin kasa da watanni biyu. 

Matan nasa su ne; Mariam Anako, wanda yanzu ita ce matarsa, Satumba 6, 2022; Elizabeth Akinmudai; Tobiloba Philips, Oktoba 9, 2022, Ashley Adegoke, Oktoba 14, 2022 da Ronke Ademiluyi, Oktoba 20, 2022.

© Daily Nigerian Hausa.

Post a Comment

Previous Post Next Post