![]() |
| Details from Facebook |
Don haka kamfanoni suke tururuwar saka tallunkansu a facebook. An bayyana cewa a shekarar 2017 facebook ya samarwa kamfaninsa cinikin dala zambar dubu sau dubu 40 wadanda kashi 89% duk daga tallace - tallace ya samu.
Saboda haka ne ake ta sukar kamfanin kasancewar ya zama kaza ci-ki-goge-baki. Duk dumbin kudin da maziyarta amma ba ya ba su ladan gaben komai alhali ga wasu da ba su kai shi ba suna gutsirawa mutanensu wani abu. To don haka, sai facebook suka kawo dabarar yadda maziyartansu za su rika samun kudi kamar yadda youtube ke yi.
Hanyoyi biyu ne ake samun kudi ta facebook. Hanya ta farko ita ce hanyar saka talla a bidiyo wanda suke kiransa 'Ad break'. Hanya ta biyu kuma shi ne tsarin saka talla a website ko manhajar android da IOS. Shi kuma suna kiransa 'Facebook Audience Network.' A karkashin akwai talla iri uku; Banner Ad, Interstitial Ad da kuma Native Ad. Fahimtar wadannan na da muhimmanci wajen sanin dabarun da famfon kudin zai yi ta kwararowa.
Wannan gabatarwa ce. Da yardar Allah zan yi rubutu daga kashi 6 zuwa 12 wadanda a ciki zan yi bayani dalla - dalla yadda ake samun kudi daga facebook.
Zan cigaba.
Daga Salisu Abdurrazak Saheel
