Daga Dr Saliadeen Sisey
Sarki Charles na uku zai sayar da wasu daga cikin dawakan da ya gada daga mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth II.
Marigayiya Sarauniya ta kasance m
ai son dawaki kuma tana kiwonsu.
Gidan gwajon kayayyaki na Tattersalls ya ce zai yi gwajon dawaki 14 na Sarauniya a yau Litinin.
Daga cikin dawakin har da Just Fine wanda ya lashe tsere kusan 100.
Kakakin gidan gwajon na Tattersalls ya ce ba wani sabon abu bane saboda a duk shekara suna sayar da dawaki.


