Daga Abdurrazak Salisu Saheel
Akwai wani tsari da kamfanin META suke daf da zuwa dashi wanda kuma masu tsarin Professional Mode ne kawai zasuci moriyarsa, wasu Stars ne kamfanin zasu samar wanda mutum zai iya siya a wurinsu, amfaninsa shine duk wanda kaga ya wallafa wani video da ya burgeka zaka iya danna masa stars daga cikin waɗanda ka siya a wajen Facebook.
Shi wannan Stars ɗin kamar dai wata ƙyauta ce zaka yi ma duk wanda kaga Video nashi ya birgeka don ƙarfafa masa giuwa. Misali kamar mu masu koyar da Fasaha zamu iya yin video na koyar da wani ilimin fasaha da zaran ya birgeku duk ƙoƙarinku shine ku danna mana wannan Star ɗin, kunga kenan a maimakon Class da muke buɗewa kuna biyan kuɗi zamu dawo kawai mu dinga sakin Video kuna danna mana Star a madadin wannan kuɗin da zaku biya na Register, Duk Star guda 100 da mutane suka danna maka zasu baka wani point mai kusan kimar $1.
Amma a yanzu wannan tsarin ba a ko wacce kasa yake available ba, sai dai daf yake da ya mamaye duniya, domin idan bazaku manta ba haka farkon fitowar FACEBOOK LIVE shima a wasu kasashe ya fara aiki kafin ta shigo kasashen mu.
Allah Ya Dafa Mana..
