An kama wata mata 'yar Najeriya ɗauke da sinadarin hodar Iblis a filin jirgin kasar Pakistan



Daga Comrd Yusha'u Garba Shanga


Hukumar yaƙi da safarar miyagun kwayoyi (ANF) Pakistan ta gano kafsul ɗin da ke cike da hodar iblis daga cikin wata mata ‘yar Najeriya da ke fasinja a filin jirgin saman Lahore a wani samame da ta kai.


A cewar rahoto a ranar Juma’a, 18 ga Nuwamba, 2022, ‘yar Najeriyar da ba a bayyana sunanta ba ta isa Lahore daga jirgin Qatar mai lamba QR-628 ta Doha.


An kama wanda ake tuhuma kuma an yi rajistar shari'a a ƙarkashin dokar hana shan miyagun kwayoyi yayin da aka fara bincike.

Post a Comment

Previous Post Next Post