Matashi Ya Kai Iyayen Budurwan Shi Kotu Saboda Zasu Aurar Da Ita Ga Wani A Kano.

Daga Abdulnasir Yusuf Ladan

Wani matashi mai suna Imam yayi karar iyayen budurwan shi a gaban babban kotun shari'an musulunci da ke hotoro a kano, inda yake neman kotun ta hanasu aurar da ita ga wani saurayin daban.

Matashin mai suna Imam Mukhtar Dala yayi karar budurwan tashi mai suna Muhassin Auwal Dala da mahaifinta AA Dala, da kakanta Sani Mai Alawayyo, da kuma aminin babanta Alhaji Audu, inda ya nemi kotu da ta dakatar da auran da ake kokarin yimata saboda shine yayi hidiman da zai aure ta.haka kuma ya nemi a hana Muhassin Dala zuwa wurin kowane mutum don daura mata aure.

Alkalin kotun mai shari'a Isa Salisu kura, ya saurari korafin wannan matashi kuma ya dage sauraron karan zuwa ranan 30 ga nuwamban nan.

Inuwar Labarai RPT 001

Post a Comment

Previous Post Next Post