Daga Comrd Yusha'u Garba Shanga
Rahotanni sun bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu, a ranar Alhamis, ya samu kambun sarauta a jihar Ebonyi.
Tinubu ya samu taken, “Dike Di Ora Nma 1 na jihar Ebonyi” gabanin taron yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, wanda aka shirya gudanarwa ranar Alhamis a filin wasa na garin Pa Ngele Oruta dake babban birnin jihar.
A cewar Chooks Oko, mai taimaka wa gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, an baiwa Tinubu laƙabin ‘Dike Di Ora Nma’ wanda ke nufin ‘Jarumin da jama’a ke so.
An gudanar da taron ne a yayin wani taro da aka gudanar a ranar Laraba a jihar.
Haka kuma wani mai goyon bayan jam’iyyar APC, DOlusegun, ya wallafa wani hoton Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC sanye da cikakkiyar rigar ƙabilar Igbo a gefensa inda wasu mata suka gabatar da wata kyauta da aka lullube, ɗauke da taken, “Asiwaju ya yi wa sarautar a jihar Ebonyi.
"Yanzu Shine DIKE DI ORA NMA 1 Na Jihar Ebonyi."
